ABUBUWAN DAKE HADDASA ZUBEWAR GASHI, DA YADDA ZA A MAGANCE

Zubewar Gashi, abubuwan dake haddasa shi da yadda za a magance

A yau bayani ne dangane da zubewar gashi wato hair loss a turance, ko kuma Alopecia a yaren likita na nufin wani yanayi da mutum kan tsinci kansa na zubewa ko raguwar adadin gashin kansa akalla kwaya 100 a kullum ahankali ahankali tare da kakkaryewarsa, ko ganin ya taho makale jikin abun tace kai, ko kuma ma mutum ya samu kansa gaba daya babu gashin ko gashin ya zube ya mai dashi mai sanko aka. Baya zuwa da wani zazzabi, ciwon kai ko kuraje.

Yanayi ne dakan faru ga maza da mata, manya da yara. ma’ana de ba wanda matsalar ta bari in ana maganar jinsi saide duk da hakan bakowa ke haduwa da matsalar ba sannan akwai wasu abubuwa na daban dake kara kusanta wasu da larurar.

Ire iren zubewar gashi

  1. Akwai zubewar gashi baki daya naka wato (alopecia totalis)
  2. Akwai zubewar gashin iya kai wanda yake tsalmi tsalmi kamar makero
  3. Akwai zubewar gashin kai hade dana jiki baki daya wato ko ina mutum ya rika ganin ba gashi jikinsa musamman gashin gira, gemu a maza, ko gashin ido (Alopecia universalist)

Abubuwan da suke kawo hakan

Takamai mai ba asan meke jawo hakan ba amma de akwai wasu abubuwa daban daban wadanda suka hada da;

  1. Kwayoyin halitta na gado, wato wasu suna gadar hakan ne daga iyaye ko kakanni sakamakon wani sindarin halitta dasu magabatan suka rasa, irin wannan zubewar gashin muna kiransa da (alopecia areata)
  2. Akwai zubewar gashi sakamakon kwayoyin garkuwar jikin mutum dake bashi kariya ta hanyar yaki da kwayoyin cuta ajika wanda akarshe suke komawa su rika cin sinadaran dake samar da gashin bisa kuskuren cewa kwayoyin cutane suka shigo jiki alhalin ba haka abun yake ba. Wato (Auto immune)
  3. Sai zubewar gashi sanadiyyar karancin sinadarin rayuwa dake taimakawa fitowar gashi da ake kira (androgen) a turance.
  4. Zubewar Gashi sakamakon haduwa da wata larura dake bukatar shan magani akai akai musamman masu ciwon suga, ciwon makoko (thyroid problems), maganin ciwon sanyin kashi wato ciwon guiwoyi hannu da kafa, maganin hawan jini, da ciwon cancer, abune da yake common atsakaninsu.
  5. Sai zubewar gashi ko sanko musamman ga maza sakamakon yawaitar sinadarin testestorone ajika.
  6. Idan mutum na kar6ar radiation therapy aka, wato amfani da zafi yayin kone wasu kwayoyin cuta ajika akan mutum musammn cutar kansa.
  7. Sai canjin sinadaran halitta wanda hakan kan faru ne kurum.yayin da mace ta sami juna biyu cimma shekarun dena haila ko bayan anhaihu.
  8. Sai fama da stress wato matsananciyar damuwa afili ko kuma acikin ciki wato physical or emotional stress
  9. Yawan canza salon kitse kitse da gyare gyaren gashi.
  10. Wadannan sune mahimman abubuwan da suke jawo zubewar gashi.
  11. Wadanda zasu iya samun kansu a cikin irin Wannan matsalar
  12. Mahimmin abunda ke jawo mutumin ya fuskanci zubewar gashi shine Gado (genetic predispositions) idan har acikin dangi ko aka sami mahaifiya kanta ta ta6a ko tayi fama dashi toh kema amatsayin ya’ zaki iya gada. Idan akace gado basai iyaye wanda kasani ba hatta kakarki ta 10 dako a tarihi mamarki ko babanki ma basu san zancenta ba kina iya daukowa daga ita ta hanyar iyayenki walau dangin uwa kona uba. Kuma wannan shike dauke da kaso 85% cikin dari.
  13. Sauran 15% din duk kurum sun taru ne a:
  14. Shekaru a wato shekarun tsufa, a lokacin tsufa abune da yake normal ba larura ba dan anga gashi na zubewa, haka kuma a musamman macen data fara manyanta ta cimma shekarun dena haila shekara 40 zuwa 50 aduniya.
  15. Kasancewa cikin damuwa koda yaushe (stress)
  16. Me fama da ciwon suga
  17. Me dauke da ciwon cancer
  18. Mutumin da kullum yake kara ramewa haka kurum
  19. Karancin ingantaccen abinci ajika wato mutum mai dauke da ciwon yunwa.
  20. Matakan kariya daga karairayewa gashi
  21. Abubuwan da mutum zai taimaki kansa musamman mai larurar ko wanda ma baida ita kuma baya fatan ya kamu sune:
  22. Wajibine mai wannan matsalar ya kauracewa shan taba ko inda ake shanta
  23. Post din yayi tsawo zan cigaba Insha Allah

Join Our Whatsapp Group

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Check Also
Close
Back to top button
error: Alert: Content selection is disabled!!