SHIN KO KASAN YADDA ZAKA RAGE YAWAN SHAN DATA/MB A WAYOYIN ANDROID CIKIN SAUKI?

Mutane da yawa, musamman masu amfani da manyan wayoyi na zamani,kamar wayoyin Android sukan koka akan yanda datarsu ke saurin karewa da zarar sun yi
subscription. Wannan dalili ne ke sanya wasu ma kan bar yawan bude datar ko kuma ma su rabu da
wayar baki daya.

Wannan abu ba hakanan kawai yake faruwa ba, akwai dalilai da kan sanya hakan.

A cikin wannan darasin namu, zamu yi tsokaci akan wadannan dalilan da kuma yanda zaku shawo kan wannan matsala ta yawan shan data. Sanin kowa ne a wannan lokaci da muke ciki, kusan dukkanin wayoyin da muke amfani da su, musamman ma manya wayoyi, mafi yanwancin aiyukansu sun dogara ne akan internet. Wannan dalili ne ya sanya cewa, idan har mutum baya da data a cikin layinsa, to sai ka ga ya kasa yin wasu da yawa daga cikin muhimman ayyukan da wadannan wayoyin kan yi. Saboda amfanin da wadannan wayoyin ke yi da
data ne ya sanya aka basu damar cewa, da zarar mutum ya kunna data, to su ci gaba da yin wasu
muhimman aiyuka ba tare da sun sanar da mai wayar ba (wato background data).

Wasu wayoyin kuma application din su ne ke yin update lokaci zuwa lokaci domin inganta ko kuma sabinta
yanayin yanda wayar ke aiki. Wani lokacin kuma, applications din da mutum ke yin installing a cikin
wayar ne ke amfani da wannan damar domin yin wasu ayyukan da ke bukatar data ba tare da sun nemi izinin mai wayar ba.

Shin ko kana cikin wadanda ke fama da irin wannan matsala ta shan data?

To kwantar da hankalinka, ga hanyoyin da zaka bi domin ragewa
ko kuma tsaida wannan shan data da wayarka take yi. Background Data App background data shine babban abin da ke sanyawa waya ta rika shan data babu gaira babu
dalili! Duk da cewa wayoyi da yawa na zuwa da wannan tsarin, wayoyin android sun fi kaurin suna
akan wannan matsala. To sai dai, duk da haka, wayoyin android din suna bada dama ga mutum
domin ya zabi applications din da yake bukatar ya rika amfani da data a ko da wane lokaci, tare da
kuma tsayar da wasu application din daga yin amfani
da data ba tare da saninshi ba.

Domin gane ko wane application ne yake shan
data ba tare da saninka ba, to sai ka shiga cikin
Settings na wayarka, ka duba daga kasa kadan, zaka ga inda aka sanya Data Usage . Idan ka shiga wurin zaka ga list na duk application da ke amfani da datarka, idan kaga akwai wani wanda baka
yarda da shiba to zaka iya hanashi yin amfani da data har sai ya samu izininka.

Domin tsaida
application daga shan data kai tsaye, sai a bi wadanna matakan:

  • 1.Shiga cikin settings
  • 2.Duba daga kasa kadan, akwai inda aka sanya
  • Data Usage
  • 3.Idan ka shiga Data usage , zaka ga list na applications din da ke shan data da kuma yawan
  • datar da suka sha
  • 4 . Domin tsaida application daga shan data, sai ka taba application din, nan take wani page zaya bude.
  • 5 . Sai ka duba daga kasa, akwai inda aka sanya Restrict app background data , sai ka taba ko kuma ka kunna.
  • Haka zaka yi ma duk wani application da kake
  • bukatar takaita yanayin shan datar da yake awayarka. Daukar wadannan matakan kadai, zaya
  • taimaKa maKa wajen rage yanayin yanda wayarka ke sha maka data sosai. Wannan sune hanyoyi da zaka bi domin rage yawan data da wayarka ke amfani da ita ba tare
  • da saninka ba.

Join Our Whatsapp Group

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
error: Alert: Content selection is disabled!!